Isa ga babban shafi
Faransa

Macron zai sake cinikin tashar gina jiragen ruwan Faransa

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce gwamnatin sa zata bukaci sake cinikin tashar gina jiragen ruwan da aka sayarwa wani kamfanin Italiya domin kare ayyukan 'yan kasar.

Shugaba Macron na Faransa a lokacin da ya ziyarci tashar gini jiragen ruwan Saint Nazaire
Shugaba Macron na Faransa a lokacin da ya ziyarci tashar gini jiragen ruwan Saint Nazaire REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Shuagban da ya ziyarci tashar, ya ce ministan kudi Bruno Le Maire zai tattauna kan sake fasalin cinikin da kuma yadda gwamnatin zata rike wani kashi na kamfanin da ke Saint Nazaire.

Tsohuwar gwamnatin Francois Hollande ta sayar da tashar kerar jiragen ruwan akan kudi Dala miliyan 89 dan karbe kasha 67 na hannayen jarin sa.

Akalla ma’aikata 2,600 ke aiki a tashar tare da wasu 5,000 yan kwantiragi.

A wani labarin kuma Shugaban ya bayyana goyan bayan sa ga ministan kula da yankunan kasar Richard Ferrand da ake zargi da karya ka’idar aiki, inda ya bukaci kafofin yada labarai da kada suyi saurin yanke hukunci kan lamarin.

Ana zargi ministan ne da fifita matar sa wajen wani aikin da ya shafi inshoran kula da lafiya lokacin da ya jagoranci kamfanin.

Ministan ya yi watsi da zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.