Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka: An fara bincikar kwamitin yakin neman zaben Trump

Kwamitin majalisar dattawan Amurka da ke bincika zargin da ake wa kasar Rasha na sanya hannu cikin zaben shugabancin Amurka a shekara ta 2016, ya umarcin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar Donald Trump, da ya mika masa baki dayan takardun da suka shafi kaddamar da yakin neman zaben da yayi a watan Yunin shekara ta 2015.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS
Talla

Jaridar Washington Post ta rawaito cewa, majalisar dattijan Amurkan, na bukatar abubuwan da suka shafi, dukkanin musayar sakwannin e-mail, da baki dayan bayanan wayar tarho na jami’an kwamitin yakin neman zaben da aka nada tun bayan kaddamar da yakin neman zaben.

Karo na farko kenan da aka shigo da kwamitin yakin neman zaben Trump kai tsaye cikin binciken da ake yi na zargin hadin bakin Rasha da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar a shekarar da ta gabata.

Nan da wani lokaci ne ake sa ran gayyatar da dama daga cikin jami’an da suka gudanar da aikin yakin neman zaben Trump domin yin karin haske kan abinda suka sani kan zargin da ake musu agaban zauren majalissar dattijan kasar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.