Isa ga babban shafi
Britaniya

Britaniya ta dauki sabbin matakan tsaro

Birtaniya na shirin baza sojoji sassan kasar domin tabbatar da zaman lafiya da kuma samar da tsaro bayan kazamin harin da aka kai Manchester wanda ya hallaka mutane 22.

Friministan Britaniya Theresa May
Friministan Britaniya Theresa May REUTERS/Toby Melville
Talla

A jawabin da ta yiwa al’ummar kasar, Firaminista Theresa May, ta ce lalle akwai barazanar kai Karin hari kuma akwai alamun da ke nuna cewar kungiyoyin da ke shirya harin na da yawa.

Jawabin na ta na zuwa ne bayan an bayyana wani dan assalin kasar Libya Salman Abedi a matsayin wanda ya kitsa harin na Manchester.

Batun da ke zuwa bayan Kungiyar ISIS, ta ce ita ke da hannu wajen kai harin.

Babu cikakken bayanai kan Matshin mai shekaru 22, sai dai majiyoyin tsaron yankin da aka kai harin sun ce iyayyensa ‘yan asalin Libya ne wanda mulkin Moamer Kadhafi ya tilsastawa tserewa daga kasar.

Theresa May ta lashi takobin yakar ta’addanci wanda ta ce ba zai hana wanzuwar kasar ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.