Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela: Sama da mutane dubu 200 sun sake fita zanga zanga

Dubban ‘yan kasar Venezuela ne suka mamaye titunan kasar, domin bikin cika kwanaki 50, da kaddamar da gagarumar zanga zangar neman shugaban kasar Nicolas Maduro ya sauka daga mukaminsa.

Wani yanki na hoton dubban 'yan kasar Venezuela da suka fita zanga zangna
Wani yanki na hoton dubban 'yan kasar Venezuela da suka fita zanga zangna REUTERS/Christian Veron
Talla

A wannan karon, sama da mutane dubu 200 ne suka gudanar da zanga zangar, sai dai wani kakakin masu zanga zangar, Edinson Ferrer, ya ce, a birnin Caracas kadai, akalla mutane dubu 160 ne suka fita.

‘Yan kasar dai na neman Maduro ya sauka daga shugabancin kasar ne, saboda gazawar da suka ce yayi wajen magance hau-hawar farashin kayan abinci, karancinsa da kuma tsadar magunguna.

dan takarar shugabancin kasar ta Venezuela, kuma madugun 'yan dawar kasar Henrique Capriles  ne ya jagoranci gudanar da gagarumar zanga zangar a wannan lokaci, kuma yayin jawabin da ya yiwa dubban masu zanga zangar, Cariles ya koka bisa yadda ya ce gwamnatin Maduro na cigaba da take hakkin dan adam, duk da gazawar da ta yi wajen magance matsalar tattalin arzikin da ke damun yan kasar.

Zuwa yanzu, masu zanga zanga 50 ne suka rasa rayukansu, cikin kwanaki 50 da 'yan kasar suka shafe suna neman tilasta kawar da gwamnatin Maduro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.