Isa ga babban shafi
Amurka

Ina da 'yancin musayar bayanai da Rasha - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya jaddada cewa yana da ‘yancin musayar wasu bayanan sirri yayin tattaunawa da wakilan kasar Rasha.

Shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington.
Shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Da’awar ta Trump, na zuwa ne kwana guda, bayan bullar rahotannin cewa, shugaban yayi musayar wasu bayanan sirri da manyan jami’an Rasha, yayin wata ganawa da suka yi a Amurka a kwanakin baya.

Rahoton da jaridar Washington Post ta wallafa ya bayyana cewa Shugaba Trump ya sanar da Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov wasu muhimman bayanai dangane da mayakan IS yayin wani taro tsakaninsu a makon daya gabata, wanda shi ma jakadan kasar Rasha a Amurkan ya samu halarta.

To sai dai a yau Talata ta shafinsa na Twitter Trump ya yi Karin bayanin cewa bayanan da ake ta yi masa kwarmaton bai kamata ya tattauna da Rasha ba, batutuwa ne da suka shafi yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da cewa ‘yan ta’adda ba su yi amfani da sufurin jiragen sama ba wajen cimma manufofinsu, don haka yana da damar tattauna da Rasha kasancewar manufarsu guda kan yakar ta’addanci.

Shi kuwa kakakin gwamnatin Rasha Dimtri Peskov bayyana zargin yayi da maganar da bata mcancanci su karyata ko kuma su tabbatar ba saboda rashin muhimmancinta

a sharhin da suka yi masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro sun bayyana matakin na Trump da cewa bai sabawa doka ba sai dai akwai hadarin fitar da bayanan sirrin ka iya haifarwa shirin Amurka wajen yaki da ta’addanci koma baya.

Bada dadewa bane gwamnatin Trump ta haramta daukar Na’urar Komfutar tafi da gidanka a jiragen saman fasinjoji daga wasu kasashen gabas ta tsakiya domin dakile Duk wani yunkuri na ‘yan ta’adda don amfani da wannan dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.