Isa ga babban shafi
Amurka-Turkiya

Anya yunkurin Erdogan na kyautata alaka da Amurka zai yi nasara?

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a fadar White House, bayan da ya isa kasar.

Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan, tare da mai dakinsa Emine Erdogan, yayin da suka sauka a birnin Washington don ganawa da shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Turkiyya Tayyip Erdogan, tare da mai dakinsa Emine Erdogan, yayin da suka sauka a birnin Washington don ganawa da shugaban Amurka Donald Trump. Reuters/路透社
Talla

Taron tsakanin shugabannin biyu, ya zo ne bayan nasarar da Erdogan yayi a zaben jin ra’ayin jama’ar kasarsa da aka yi, kan daga likkafarsa zuwa shugaban kasa mai cikakken iko.

Ana sa ran tattaunawar da ake yi tsakanin shugabannin biyu, ta yi tasiri wajen maido da kykkyawar dangantaka tsakanin Amurka da Turkiya, wadda a baya ta yi tsami bisa batutuwan da suka diflomasiyya, musamman kan kasar Syria da kuma cigaba da zaman malamin addini Fethullah Gullen a Amurkan da Turkiya ke zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba a Shekarar da ta gabata.

A zamanin mulkin Barrack Obama dangantaka ta yi tsami tsakanin Amurka da Turkiya musamman kan zargin da Turkiyan ke mata na marawa mayakan Kurdawa da ke yaki a kasar Syria baya ta hanyar basu makamai, wadanda ta ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda.

Kafin tattaunawar ta yanzu shugaban Turkiya Recep tayyib Erdogan, ya bayyana a fili cewa yana sa ran gwamnatin Trump ta mika masa Fethullah Gullein da yake zargi da yunkurin yi masa juyin mulki, bukatar da masu sharhi suka yi gargadin cewa ba abu bane mai sauki Trump yayi wannan alkawarin la’akari da sarkakiyar dokokin Amurka kan wannan bukata.

Bayan kammala taron ne ake sa ran Trump da Erdogan su ganawar hadin gwiwa da ‘yan jaridu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.