Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya zabo sabbin jini a Jam’iyyarsa

Jam’iyyar Shugaban Faransa mai jiran gado Emmanuel Macron ta fitar da sunayen mutane sama da 400 wadanda za su tsaya takara a zaben ‘yan majalisu da za a gudanar watan Yuni mai zuwa.

Emmanuel Macron hugaban Faransa mai jiran gado
Emmanuel Macron hugaban Faransa mai jiran gado REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kusan rabin mutanen sabbi ne a siyasar Faransa wadanda ba su taba tsayawa takarar zabe ba.

Sabuwar Jam’iyyar Macron da aka kafa watanni 13 da suka gabata na tattare da kalubalen ganin ta samu rinjaye a kujeran majalisu domin fafatawa da manyan jam’iyyun siyasar kasar.

Wannan ne karon farko da aka samu wata sabuwar jam’iyya da ta lashe zaben shugaban kasa a Faransa bayan shafe shekaru kusan 60 jam’iyyun siyasa biyu na mulki a kasar.

Kashi 52 na wadanda za su tsaya takara a jam’iyyar Macron sabbin fuskoki ne a Siyasa, kuma kashi 50 duk mata ne.

Daga cikin mutanen da Macron ya zabo akwai mai shekaru 24, kuma kusan mutane 10 daga cikinsu ba su da aikin yi wadanda suka kunshi har da dalibai da wadanda suka yi ritaya.

Akwai ‘Yan majalisa 24 ‘yan Jam’iyyar Hollande ta Socialist da Macron ya zaba, wadanda ya ke bukatar su sake tsayawa takara a jam’iyyarsa.

Tuni dai tsohon Friministan kasar Manuel Valls ya bayyana kudirin yin tafiya tare da Macron a sabuwar Jam’iyyar shugaban mai jiran gado, matakin da aka yi watsi da shi.

Macron yanzu na bukatar Karin mutane 100 da za su tsaya takara a sabuwar jam’iyyarsa domin samun rinjaye a Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.