Isa ga babban shafi
Faransa

Zaben Macron Kamar “Da rashin uwa ne ake yin uwar daki”

Nasarar Macron a zaben shugaban kasar Faransa da aka gudanar a ranar Lahadi ba ta bai wa mafi yawan Faransawa mamaki ba, sai dai watakila mamakin shi ne nasarar doke 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasar kasar tun a zagayen farko da aka gudanar a ranar 23 ga watan jiya.

Magoya bayan Emmanuel Macron a Louvre
Magoya bayan Emmanuel Macron a Louvre ©Pierre René-Worms
Talla

Amma kafin tabbatar da samun nasarar, akwai muhimmin abu da suka yi matukar daukar hankulan jama'a wanda ya fara haifar da fargaba ga Faransawa da kuma sauran kasashe musamman a yankin Turai, wannan kuwa ba wani abu ba ne face yiyuwar samun karancin masu kada kuri’a.

An yi hasashen cewa Idan hakan ta faru, to kai tsaye zai shafi bangaren Macron ne, domin a tarihi magoya bayan jam'iyyar Front National ba a san su da kaurace wa rumfunan zabe ba.

Alkalumman dai na nuni da cewa sama da kashi 24 cikin dari na jama'ar da suka cancanci kada kuri’unsu ne suka kaurace wa zaben, lamarin da ke da matukar tasiri ga kimar da ake bai wa shugaban kasa a Faransa.

Wannan ne dai karo na farko da aka samu karancin fitowar jama'a makamancin haka tun bayan zaben shekarar 1969 inda da kyar aka samu fitowar kashi 68 cikin dari na jama'a a lokacin.

Wani abu a game da zaben na jiya shi ne samun kuri'un da suka lalace da yawansu ya haura milyan hudu da rabi, wadanda ko dai an yaga su da gangan, ko an yi rubutu a kansu ko kuma an sanya kuri'u biyu a cikin ambulam daya.

To ko meye dalilin haka?

Wasu dai na danganta lamarin a matsayin nuna fushi da kayan da 'yan takarar da suke kauna shuka sha a zagayen farko.

Wasu daga cikinsu na cewa ba za su iya zaunawa gida a ranar zabe ba, sannan kuma ba za su bai wa Emmanuel Macron ko kuma Marine Le Pen kuri'unsu ba saboda manufofinsu sun yi hannun riga da abin da suke bukata.

To sai dai akwai wadanda ke kallon nasarar da Macron ya sama akan Le Pen da cewa ba wani abu ne ya haifar da ita face abin da Hausawa ke cewa da rashin uwa ne ake yin uwar daki, ma'ana dai dole ne a fito domin kada masa kuri'a, idan ba haka ba kuwa ragamar mulkin kasar ce za ta fada hannun 'yar takarar masu zazzafan ra'ayi.

Kasashen duniya da dama ne suka yaba da galabar da Macron ya samu, cikin har da shugannin kasashen duniya irinsu Amurka da Jamus da Birtaniya da dai sauransu.

Galabar Macron dai na a matsayin gagarumar galaba ga kungiyar Turai baki daya, lura da irin alkawurran 'yar takara Marine Le Pen ta dauka na tabbatar da cewa Faransa ta fice daga wannan kungiya idan har ta yi nasara a zaben duk kuwa da matsayi da kuma tarihin Faransa a kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.