Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya za ta hakura da shiga Tarayyar Turai

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya gargadi Tarayyar Turai cewa zai yi watsi da bukatar shiga kungiyar da kasarsa ta shafe lokaci tana nema. Shugaban ya ce Turkiya na iya hakura da bukatar idan har babu fahimtar juna tsakaninsu.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

Shugaban Erdogan ya ce babu wani lokaci da ya wuce yanzu da Tarayyar Turai za ta amince da bukatar Turkiya na zama mambar kungiyar.

A cewar shugaban idan har kudirin ya wuce yanzu to kasarsa ta hakura, sai su ce a sauka lafiya.

Erdogan ya bukaci Tarayyar Turai ta cika alkawullan da ta dauka a jarjejeniyar baya da suka kulla, kafin hawa teburin tattaunawa.

A cewarsa yanzu babu wani abu da ya rage su tattauna.

Tun 1960 Turkiya ke fadi tashin shiga Tarayyar Turai, kuma ta sha kulla yarjeniyoyi domin cim ma bukatar amma hakarta ba ta cim ma ruwa ba .

Shugaban na Turkiyan ya fadi haka ne dai bayan sake zama mamba a jam’iyyarsa mai mulki ta AKP bayan shafe shekaru uku baya jam’iyyar saboda tsarin kasar da ya tilastawa shugaba raba gari da jam’iyyar siyasa.

Yanzu kuma kundin tsarin mulki da aka sauya wanda ya kara masa karfin iko ya ba shi damar zama mamban wata jam’iyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.