Isa ga babban shafi
Faransa

Macron da Le Pen sun halarci jana’izar Dan sandan da IS ta kashe a Paris

‘Yan takara biyu da ke gwagwarmayar zama shugaban kasa a Faransa, Emmanuel Macron da Marine Le Pen sun halarci jana’izar dan sandan da aka kashe a harin Champs Elysées, a daidai lokacin da yakin neman zaben ‘yan takarar biyu ke mayar da hankali ga barazanar tsaron Faransa.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya jagoranci gangamin karrama Dan sandan da IS ta kashe a Paris
Shugaban Faransa Francois Hollande ya jagoranci gangamin karrama Dan sandan da IS ta kashe a Paris REUTERS
Talla

Macron da Le Pen suna cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana’izar a yau Talata birnin Paris wanda Shugaban kasa Francois Hollande ya jagoranta.

Harin na Champs Elysée da aka kashe dan sandan Faransa a ranar Alhamis a daidai lokacin da ‘Yan takara ke muhawara ya kasance madogara ga Marine Le Pen mai tsatstsauran ra’ayin rikau.

Kungiyar IS da ke da’awar jihadi ta dauki alhakin kai harin wanda ya kashe dan sanda Xavier Jugele kwanaki uku a jefa kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na farko.

‘Yan takarar biyu dai nada sabanin ra’ayi game da manufar tsaron Faransa da ke fuskantar hare haren ta’addanci tun 2015 inda mutane kusan 250 suka mutu zuwa yanzu.

Le Pen na da ra’ayin karbe ragamar kare iyakokin Faransa daga Tarayyar Turai tare da taso keyar baki daga kasashen da ke fama da hare haren ta’addanci.

Amma Macron ya sha alwashin tabbatar da huldar Tarayyar Turai domin karfafa matakan tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.