Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya goyi bayan Macron

Shugaban Faransa Francois Hollande ya sanar da matakin marawa Emmanuel Macron baya a zaben shugaban kasa zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 7 ga Mayu, tare da bayyana hadarin da ke tattare da zaben Marine Le Pen mai tsattsauran ra’ayin rikau.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande Reuters
Talla

Hollande ya ce Macron zai kada wa kuri’arsa tare da bayyana cewa zaben Le Pen barazana ne ga makomar Faransa a Tarayyar Turai.

Macron dai ya taba rike mukamin Ministan tattalin arziki a gwamnan Hollande, amma a watan Agusta ya fice gwamnatin.

Wannan ne karon farko da Macron ya tsaya takara a siyasar Faransa wanda ya kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa cikin watanni 12.

Sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a na ci gaba da tabbatar da cewa Macron ne zai lashe zaben a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.