Zaben Faransa: Macron da Le Pen za su fafata a zagaye na biyu
Sakamako daga rumfunan zaben kasar Faransa ya nuna cewa, dan takar mai zaman kansa Emmanuel Macron ne ke kan gaba a kuri’un da aka kada a zagayen farko na zaben shugabancin kasar da aka gudanar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mai ra’ayin kishin kasar ta jam’iyyar National Front Marine Le Pen ke biye da Macron a matsayi na biyu, wanda hakan ya ba su damar zuwa zagaye na biyu za a yi a ranar ga 7 ga watan Mayu mai zuwa.
Macron na da kashi 23 zuwa 24 na kuri’un da aka kada yayin da Le Pen ke da kashi 21 zuwa 23.
Masu hasashe dai na ganin cewa Emanuel Macron mai shekaru 39 zai iya lashe zaben shugabancin Faransa, wanda sakamakonsa ke da tasiri kan Kungiyar Tarayyar Turai EU.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu