Zaben Faransa: An tsaurara matakan tsaro
Faransa ta shirya tsaf domin kada kuri’ar shugaban kasa, sai dai har yanzu babu hasashen wanda zai iya nasara, al’amari irinsa na farko a tsawon shekaru.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce yau jajibirin zaben, an tsaurara matakan tsaro, yayin da ake ci gaba da furgaban harin ta’addanci bayan kashe dansanda a birnin Paris.
Akasarin al’ummar kasar har yanzu basu tsayar da wanda zasu jefa wa kuri’ar ba, kana bincike ya nuna cewa Faransawa da dama sun fi damuwa da batun samar da ayyukanyi da habbaka tattalin arziki kan ta’addanci.
Mutane 2 da sukayi nasara a zaben na gobe, sune zasu fafata a zagaye na gaba da za’a gudanar 7 ga Mayu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu