Hukumomin Faransa na bincike kan maharin Paris
Masu shigar da kara a Faransa na binciken asalin maharin da ya kashe jami’in ‘yan sanda guda a wani hari da ya kaddamar a kasaitacciyar unguwar Champs Elysees da ke birnin Paris.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da zagayen farko na zaben shugabancin kasar a gobe Lahadi.
Harin wanda kungiyar ISIS ta ce ta na da hannu a cikinsa, ya janyo musayar ra’ayoyi tsakanin ‘yan takarar kan yadda za a samar da tsaro a Faransa.
Masu sharhi sun bayyana cewa, harin na ranar Alhamis da ta gabata, zai iya yin tasiri dangane da fitowar jama’a don kada kuri’unsu a zaben.
Tuni dai jami’an tsaro suka kashe maharin mai suna Karim Cheurfi kuma dan shekaru 39.
Hukumomin tsaron Faransa za su jibge jami'an 'yan sanda dubu 50 da kuma sojoji dubu 7 don bai wa masu kada kuri'u a zaben na gobe kariya a duk fadin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu