Isa ga babban shafi
Faransa

Jean-Luc Mélenchon dan takarar zaben 2017 a Faransa

Jean-Luc Mélenchon mai ra’ayin kominisanci, na daya daga cikin mutane 11 da za su fafata da juna a zaben shugabancin Faransa ranar Lahadi mai zuwa. Yana cikin ‘Yan takara da ke bada mamaki a yakin neman zabe.

Jean-Luc Mélenchon, Dan takarar shugaban kasa a Faransa
Jean-Luc Mélenchon, Dan takarar shugaban kasa a Faransa Photo Anne-Christine Poujoulat. AFP
Talla

Tarihin Jean-Luc Mélenchon

An haifi Jean-Luc Mélenchon ne a ranar 19 ga watan Agustan 1951 a garin Tangier a kasar Marocco, kuma mahaifiyarsa ‘yar asalin kasar Spain ce. Ya fara rayuwarsa ne a Morocco kafin iyayansa su dawo da shi zuwa Faransa a 1962.

Ya yi karance-karancensa ne a makarantu da dama har zuwa jami’ar Besançon. Ya fara aikin koyarwa ne, kafin daga bisani ya shiga harkar siyasa karkashin inuwar jam’iyyar Socialist a 1976.

Mélenchon, an fara zabensa ne matsayin kansila kafin a nada shi mukamin karamin ministan ilimi a shekara 2002, kuma tun a wannan lokaci ake kallonsa a matsayin kusa daga cikin masu ra’ayin rikau a jam’iyyar ta Socialist.

Daga nan ne ya fice daga jam’iyyar baki daya inda suka samar da sabuwar jam’iyya tare da wasu mutane gagga daga Socialist irinsu Marc Dolez da kuma Martine Billard.

Jean-Luc Mélenchon ya yi nasarar shiga zauren majalisar dokokin tarayyar Turai a shekara ta 2009 sannan ya tsaya takara karo na farko a zaben shugabancin Faransa a shekarata 2012, inda ya zo na hudu da kashi 11.1%.

A zaben da za a yi ranar lahadi mai zuwa kuwa, Mélenchon yana takarar ne ba tare da ya tsaya karkashin inuwar wata jam’iyya ba, kuma yanzu haka ana lissafa shi a cikin mutane hudu da kowanne zai iya wuce zuwa zagaye na biyu na wannan zabe da mutane 11 ke shirin fafata a ranar Lahadi 23 ga Afrilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.