Isa ga babban shafi
Faransa

Manufofin 'yan takarar Faransa kan EU

Dama daga cikin hankulan Faransawa sun karkata kan dan takara mai zaman kansa Emmanuel Macron da ke da ra’ayin zaunar da Faransa a cikin kungiyar Tarrayar Turai da kuma Uwargida Marine Le Pen ta jam’iyyar National mai adawa da ci gaban zaman kasar a Turai.

Mutane 11 ne ke takara a zaben shugabancin Faransa
Mutane 11 ne ke takara a zaben shugabancin Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Matsayin ilahirin ‘yan takarar kasar 11 kan kungiyar EU da baki da kuma mu’ammala da al’ummar Musulmi na da matukar mahinmanci a siyasar Faransa.

Macron ya ce ko shakka babu, kasancewarsa cikakken Bafaranshe ya fi sha’awar hada kai da sauran kasashen Turai don ciyar da nahiyar gaba.

Ika kuwa Le Pen cewa ta yi, in har ta lashe zaben shugabancin kasar, za ta fitar da Faransa kungiyar kasashen Turai.

Shi ma Jean-Luc Melenchon da ke ci gaba da samun karbuwa, na adawa da zaman Faransa a Turai, yayin da ya ce, in har ya ci zaben, zai bukaci a gudanar da zaben raba gardama kan batun zama a EU.

Francois Fillon kuwa, da ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar Conservative, na goyon bayan Tarayyar Turai, sai dai yana adawa da salon tsarin tattalin arzikin kungiyar.

Dan takara a jam’iyya mai mulki, Benoi Hamon shi ma dai na adawa da tsare-tsaren EU duk da dai bai ce, in har ya ci zabe zai fidda kasar daga cikin kungiyar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.