Isa ga babban shafi
Faransa

'Yan ta'adda sun yi shirin kai hari a Faransa

Hukumomin Faransa sun gano kayayyakin kera bindigogi da bama-bamai bayan sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da shirin kaddamar da hari a kasar. 

Faransa ta ce za ta tabbatar da tsaro a lokacin zaben shugancin kasar
Faransa ta ce za ta tabbatar da tsaro a lokacin zaben shugancin kasar AFP/Christophe Simon
Talla

Hukumomin Faransa sun gano kayayyakin kera makaman ne a yayin gudanadar da bincike a birnin Merseille bayan matasan sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda.

Majiyoyi sun bayyana matasan a matsayin ‘yan asalin Farasnsa da suka hada da mai shekaru 23 da kuma 29.

Ministan cikin gidan Faransa, Matthias Felk ya bayyana cewa, matasan sun yi shirin kai harin nan da kwanaki kalilan masu ziuwa.

Mr. Felk ya ce, Faransa za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaben shugabancin kasar da za a gudanar a karahen mako mai zuwa.

Kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP ya rawaito cewa, an raba wa dogaran ‘yan takarar shugabancin Faransa hotunan wadannan matasa guda biyu saboda tsaro.

Kimanin mutane 230 ne suka rasa rayukansu sakamaon hare-haren ta’adddaci tun daga watan Janirun shekarar 2015 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.