Isa ga babban shafi
EU

EU na daukan matakan kare yara Bakin-haure

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da sabbin matakan da ta ke dauka don kare kananan yara  Bakin-haure da ake cin zarafi a Turai, da tsare su. Matakan da kungiyoyin kare hakkin yara suka yi naam da shi.

Yara Bakin haure na fuskantar cin zarafi a Turai inji EU
Yara Bakin haure na fuskantar cin zarafi a Turai inji EU LOUISA GOULIAMAKI / AFP
Talla

Shugaban sashin da ke kula da ‘yan gudun hijira a Kungiyar, EU, Dimitris Avaramopoulos ya shaidawa taron manema labarai a Brussels cewa daya bisa uku na masu neman mafaka a Turai yara ne da ke bukatar kulawa ta musamman.

Kana a shekarar da ta gabata akwai ‘yan gudun hijira miliyan 1.2 da aka yiwa rajista a kasashen Turai, bayan miliyan 1.26 da sukayi tururuwan shiga kasashen a 2015.

Dimitris ya ce akwai bukatar su tabbatar da cewa yara basa fuskantar barazanar cin zarafi, lalata da kuma shiga mugan hali ko ta’addanci.

Hukumar ta ce, za ta dauki matakan da suka dace wajen inganta rayuwar kananan yara.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta HRW, a Satumba shekara data gabata ta rawaito irin matsananci hali da yara ke fadawa a Turai.

Kungiyoyin kare hakkin yara na fatan a gaggauta aiwatar da shirin EU don ceto yara bakin haure daga barazanar da suke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.