Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya na kokarin karfafa diflomasiyar ta da kasashen Duniya

Firaministar Birtaniya Theresa May ta isa birnin Riyad na kasar Saudiyya domin ganawa da hukumomin kasar dangane da batutuwan da suka shafi kasuwanci dama tsaro. 

Theresa May Firaministan kasar Birtaniya
Theresa May Firaministan kasar Birtaniya Parliament TV handout via REUTERS
Talla

Uwargida May, wadda ta isa Riyad bayan ta ziyarci kasar Jordan a jiya, na kokarin samar da sabuwar alakar kasuwanci ne da Saudiyya a dai dai lokacin da kasarta ke ficewa daga Tarayyar Turai.
Masu lura da siyasar kasar ta Birtaniya sun bayyana cewa Saudiyya kasa ce da Birtaniya za ta amfana da ita tareda kulla yarjejeniyoyin kasuwanci da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.