Bamu yi wa kungiyar tarayyar turai barazana ba - Johnson
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Jonhson, ya musanta cewa gwamnatin kasar ta yi barazanar rage tallafinta kan yaki da ta’addanci a nahiyar turai muddin ba’a samar da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da kungiyar EU kafin ficewarta daga karkashinta ba.
Wallafawa ranar:
Yayin zantawarsa da jaridar Le Figaro da ake wallafawa a Faransa, Johnson ya ce bada gudunmawa wajen tabbatar da tsaro a nahiyar turai abu ne muhimmi ga Birtaniya.
Johnson ya ce Birtaniya zata cigaba da aiki tare da kungiyar tarayyar turai EU, domin kare nahiyar daga barazanar ta’addanci bayan ficewar kasar daga karkashin kungiyar.
An dai rawaito cewa, cikin wasikar da ta aikewa kungiyar tarayyar turai, Firaministan kasar Birtaniya Theresa May, ta ce mai yiwuwa ne gudunmawar kasar kan yaki da ta’addanci ya ragu, muddin ta fice daga karkashin kungiyar, ba tare da cimma sabuwar yarjejeniyar cinikayya da ita ba.
Sai dai fadar gwamnatin Birtaniya ta ce kalaman Firaministan ba barazana ba ce don tilasta biya mata bukata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu