Isa ga babban shafi
Faransa

Ziyarar karshe ta Francois Hollande a matsayin Shugaban Faransa

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande na ci ga ba da ziyarar kasashen Asia a Singapore, wadda itace ziyarar sa ta karshe a matsayin shugaban kasa.

Francois Hollande Shugaban Faransa  a Singapore
Francois Hollande Shugaban Faransa a Singapore © 2015 Présidence de la République française – Élysée.fr
Talla

Ziyarar wadda zata kai Hollande kasashen Malaysia da Indonesia zata mayar da hankali wajen kulla yarjejeniyar kasuwanci da kuma tsaro, musamman ganin muhimancin yankin dangane da habakar tattalin arziki.

Tawagar shugaban na dauke da manyan da kananan yankasuwa 40 tare da Sakataren masana’antu Christophe Sirugue da ministan tsaro Jean Yves Le Drian.

Ana saran yau shugaban zai bude wani taron yan kasuwa da yan kunshi mutane 170 kana yayi jawabi a taron Cibiyar taron Singapore.

Shugaba Hollande ya ziyarci kasashe 230 tun shekarar 2012 da ya zama shugaban kasa, kuma yanzu tafiya daya ya rage masa zuwa taron kungiyar kasashen Turai da za’ayi ranar 29 ga watan Mayu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.