Isa ga babban shafi
Amurka-Turai

Tillerson ba zai halarci taron kungiyar tsaro ta NATO ba

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya ce ba zai halarci taron ministocin harkokin wajen kungiyar tsaro ta NATO ba, wanda za’a yi a watan gobe.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson. REUTERS/Mark
Talla

Wata majiya a gwamnatin Amurka, ta ce a maimakon haka, Tillerson zai halarci taron kasashe 7 masu karfin tattalin arziki ne a Italiya, daga nan kuma ya ziyarci Rasha da nufin karfafa dangantaka.

Tuni dai aka bayyana karamin sakataren harkokin wajen Amurka Tom Shannon a matsayin wanda zai wakilci kasar a taron da kungiyar tsaro ta NATO zata yi a birnin Brussels daga ranar 5 zuwa 6 ga watan Afrilu mai zuwa.

Sai dai wata majiya daga gwamnatin Amurka da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ana sa ran a makon gobe, sakataren na harkokin wajen kasar, Rex Tillerson zai gana da wasu ministocin harkokin wajen kasashen da ke karkashin NATO, a birnin Washington.

Wannan sauyi dai ya sake karfafa shakkun da manbobin NATO ke da shi, dangane da samun cikakken hadin kai daga shugaban Amurka Donald Trump.

A watan da ya gabata mataimakin shugaban kasar ta Amurka, Mike Pence ya kai ziyara shelkawatar NATO da ke Brussels da nufin jaddada matsayar Amurka ta bai wa kungiyar hadin kai.

Sai dai Pence ya shaidawa manbobin kungiyar cewa, tilas ne kowace kasa ta kara yawan kudaden da take bayarwa a matsayin gudunmawa kan tsaro kasashe manbobin kungiyar NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.