Isa ga babban shafi
Turai

Birtaniya ta sanar da ranar da zata ficewa daga Kungiyar Turai

Kasar Birtaniya tace ranar 29 ga watan Maris zata kaddamar da aiki da sashe na 50 dake kunshe a cikin yarjejeniyar da ta samar da kungiyar kasashen Turai wanda zai bata damar ficewa daga cikin kungiyar. 

Theresa May Firaministan Birtaniya
Theresa May Firaministan Birtaniya
Talla

Firaminista Theresa May ta hannu mai Magana da yawun ta bayyana haka watanni 9 bayan al’umar kasar sun gudanar da zaben raba gardama wanda yan kasar suka zabi barin kungiyar.

Jakadan Birtaniya a Cibiyar kungiyar dake Brussels shima ya shaidawa ofishin shugaban kungiyar Donald Tusk.
Kungiyar kasashen Turai ta sanar da cewa an kamala duk wani shiri na raba hannun riga da Birtaniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.