Isa ga babban shafi
Faransa

Kotu ta fara binciken Fillon game da zargin ayyukan bogi

Kotu a Faransa ta sanar a hukumance cewa tana zargin dan takarar jam’iyyar Les Republicains a zaben shugabancin kasar na bana Francois Fillon da laifin bayar da ayyukan jabu.

Francois Fillon, dan takarar Les Republicains a zaben shugabancin Faransa
Francois Fillon, dan takarar Les Republicains a zaben shugabancin Faransa REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Lauyan Fillon mai suna Maitre Antonin Levy shi ne ya sanar da hakan, inda ya ce nan ba da jimawa ba ne wanda yake karewa zai gurfana a gaban alkalai masu bincike domin amsa tambayoyi dangane da zargin bai wa mata da kuma ‘yayansa aiki ta bayan fage.

Da farko dai Fillon ya ce matukar kotu ta fara binciken dangane da wannan batu zai janye daga takarar shugabancin kasar, to amma daga bisani ya shaida wa magoya bayansa cewa ba zai janye daga zaben ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.