Isa ga babban shafi
Birtaniya

Majalisa ta amince a fara tattauna ficewar Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta ba Firaminista Theresa May damar soma tattauna shirin ficewar kasar daga kungiyar kasashen Turai, a yayin da kuma Scotland ke barazanar ballewa daga Birtaniya.

Majalisar Birtaniya
Majalisar Birtaniya HO / PRU / AFP
Talla

Wannan zai ba Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu damar amincewa da dokar yau talata, kafin fara aiki da ita.

Hakan na nufin Firaminista Theresa May za ta fara amfani da ayar dokar Tarayyar Turai ta 50 da aka amince a Lisbon domin fara tattauna ficewa daga kungiyar.

Birtaniya dai za ta kasance kasa ta farko da ta fice Tarayyar Turai.

A watan Junin 2016 ne Birtaniya ta gudanar da zaben raba gardama, kuma kashi 52 suka amince kasar ta fice daga Tarayyar Turai yayin da 48 suka kada kuri’ar kin amincewa.

Scotland dai na cikin bangaren Birtaniya da suka kada kuri’ar ci gaba da zama a Tarayyar Turai. Yanzu kasar na barazanar gudanar da zaben raba gardama domin ficewa daga Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.