Isa ga babban shafi
Turai-Spain

An haramta wa tsohon shugaban yankin Catalan rike mukamin siyasa

Kotu a Spain ta yanke hukuncin da ke haramta wa tsohon jagoran masu fafutukar samar wa yankin Catalonia ‘yanci Artur Mas rike mukamin a ma’aikatun gwamanti har na tsawon shekaru 2 a nan gaba.

Masu zanga-zanga dauke da tutar Catalonia
Masu zanga-zanga dauke da tutar Catalonia REUTERS/Albert Gea
Talla

Mas mai shekaru 61 a duniya an same shi da laifin shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’ar yankin domin ballewa daga Spain, duk da cewa gwamnati ta gargade shi da ka da ya yi haka.

Yan aware na Catalonia a zaben baya da ya gudana sun samu nasara a yankin, lamarin da ke share fage ga yunkurinsu na ballewa daga kasar Spain.
Zabubbuka biyu ne aka gudanar a yankin na Catalonia mai yawan mutane milyan 7 da dubu dari biyar, na farko zaben ‘yan majalisa, na biyu kuwa na a matsayin kuri’ar jin ra’ayin jama’a ce game da ballewar yankin ko kuma ci gaba da kasancewa a cikin kasar Spain.
Firaministan Spain Mariano Rajoy, ya kasance daga cikin wadanda suka gudanar da yakin neman zaben kin amincewa da ballewar yankin na Catalonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.