Isa ga babban shafi
Ukraine

Karuwai na zanga-zangar neman halatta karuwanci a Ukraine

Karuwai da dama ne tare da ‘yan rajin kare hakkinsu suka fito suna zanga-zanga a yau Juma’a kan bukatar halatta karuwanci a Ukraine bayan gwamnatin kasar ta kafa dokoki masu tsauri da suka hada da cin tara ga masu sana’ar karuwanci.

Karuwai na zanga-zanga a Ukraine
Karuwai na zanga-zanga a Ukraine REUTERS
Talla

Karuwan na zanga-zangar ne a Kiev babban birnin Ukraine inda suka  rufe fuska dauke da takardun da ke cewa “Karuwanci Sana’a ce, muna adawa da haramta Karuwanci”.

Masu rajin kare hakkin Karuwan kimanin 50 ne rahotanni suka ce sun fito zanga-zangar inda suka mamaye ginin Majalisa a Kiev.

Ukraine dai ta haramta sana’ar karuwanci, tare da karbar kudade tara kimanin dala 9 ga karuwan.

Amma Karuwan sun ce suna iya biyan haraji maimakon tara da haramta sana’arsu.

‘Yan rajin kare hakkin Karuwan sun ce ‘Yan sanda na fakewa da dokar suna cin zarafin karuwan tare da karbar kudi a hannunsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.