Isa ga babban shafi
Faransa

An tube wa Le Pen rigar Kariya a Turai

Majalisar Dokokin Kasashen Turai ta janye kariyar da ‘yar takarar shugabancin Farnsa, Marine Le Pen ke da shi daga fuskantar tuhuma kan wasu hotuna da ta wallafa a shafinta na Twitter da ke nuna irin barnar da mayakan IS suka tafka.

Marine Le Pen shugabar jam'iyyar FN ta masu kishin kasa a Faransa
Marine Le Pen shugabar jam'iyyar FN ta masu kishin kasa a Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Matakin da Majalisar ta dauka zai bai wa mahukuntan Faransa damar ci gaba da tuhumar Marine Le Pen game da watsa hotunan na ayyukan IS, da suka hada da wanda ke nuna yadda kungiyar ta fille kan wani dan jaridar Amurka James Foley.

Sai dai Le Pen ta ce, wannan wani yunkurin haifar mata da cikas ne a kokarinta na neman kujerar shugaban kasa.

Majalisar ta ce matakin bai shafi zargin da ake wa Le Pen na yin almubazzaranci da kudaden jama’a bayan ta dauki mataimaki a majalisa.

Le Pen da ke takara a jam’iyyar FN ta masu kishin kasa ta sha alwashin gudanar da kuri’ar raba gardama domin ficewar Faransa a Tarayyar Turai idan har ta ci zabe.

Le Pen ta yi zargin cewa ana yi ma ta bita da kulli ne saboda manufofinta a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.