Isa ga babban shafi
Faransa

Jadot na jam'iyyar Green Party ya janye daga takarar shugaban kasa

Dan takarar kujerar shugabancin kasar Faransa karkashin jam’iyyar Green Party Yannick Jadot ya sanar da janye takararsa tare da bayar da goyon baya ga Benoit Hamon na jam’iyyar Socialist.

Yannick Jadot na jam'iyyar Green Party ya janye daga takarar shugaban kasa
Yannick Jadot na jam'iyyar Green Party ya janye daga takarar shugaban kasa REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Yannick Jadot dan rajin kare muhalli ya sanar da janye takararsa a yayin wata hira da aka yi da shi a tashar talabijin ta France 24, ya kuma ce ya yi hakan ne bayan cimma yarjejeniya da jam’iyyar Socialist.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ma dai na nuni da cewa kashi biyu cikin dari daya ne kadai ke goyon bayan Jadot.

Sannan shi ma Benoit Hamon da Jadot ya yi alkawarin marawa baya na jam’iyyar Socialist na a mataki na hudu kamar yadda kuri’ar ra’ayin jama’a ke nuni abinda ke nufin zai yi wuya ya tsallake zagayen farko na zaben shugabancin kasar.

Rahotanni na cewa Mista Hamon na lallamin Jean-Luc Melenchon domin ya janye takararsa don su hada karfi da karfe wajen ganin jam’iyyarsu ta yi nasarar zarcewa kan mulkin kasar amma kuma Melenchon ya ki amincewa da tayin.

Duk wannan na zuwa ne a yayin da ya rage makonni 7 a gudanar da babban zaben shugabancin kasar ta Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.