Isa ga babban shafi
Faransa

Anyi arangama tsakanin matasa da 'yan sanda a Paris

Wata zanga zangar da daruruwan matasa suka gudanar jiya Alhamis a birnin Paris ta haifar da taho mu gama tsakanin jami’an tsaro da dalibai.

Zanga zangar da ta gudana a birnin Paris ranar 23 ga watan Fabarairu 2017.
Zanga zangar da ta gudana a birnin Paris ranar 23 ga watan Fabarairu 2017. GEOFFROY VAN DER HASSELT / AFP
Talla

Hakan yasa ‘yan sanda suka yi amfani da karfi tare da harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa daliban.

Amfani da karfin da jami’an tsaro suka yi wajen kama wani matashi bakar fata dan shekaru 22 a duniya a farkon watan Fabrairu a Aulnay-sous-Bois, dake wajen birnin paris, ya haifar da tuhumar wani dan sanda, da aka zarga da nuna rashin imani kan matashin ta hanyar amfani da kulki, al’amari da ya jawo mahawar siyasa, da haddasa barkewar zanga zanga a Paris da kewaye, da kuma ya haifar da tashe tashen hankulla.

Wani dalibi da ya halarci zanga zangar kungiyoyin dake gwagwarmaya da nuna rashin imani da ‘yan sanda ke yi ya ce, ‘yan sanda na aikata ta’asa mai yawa a Faransa.
Zanga zangar da aka gudanar a dandalin kasa dake gabashin Paris, matasan da wasu suka rufe fuskokinsu sun yi kaca kaca da injinan cirar takardun kudin bankuna a cewar wani dan jaridar kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.

Masu zanga zangar dai sun yi yunkurin keta shingen tsaro da suka mayar da martani da harba hayaki mai sa kwalla, yayinda wasu matasan kuma ke maida martani ta hanyar jifa da duwatsu.

‘Yan sanda sun kama 11 daga cikin masu zanga zagar sata da kuma lalata dukiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.