Donald Trump ya far wa ‘yan jarida
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki kafafen yada labarai da kakkausan harshe dangane da rahotannin da suke yayatawa na alakarsa da kasar Rasha da kuma shafa wa himmarsa ta dawo da martabar Amurka bakin fenti.
Wallafawa ranar:
Donald Trump ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga taron manema labarai da ya kira a Washington.
Trump ya kuma koda nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta samu a bangaren farfado da karsashin kasuwar hada-hadar hannun jarin kasar, da kuma kamen bakin haure da ba su da takardun izinin zama a Amurka.
A cikin jawabin da ya gabatar yayin taron manema labaran tsawon mituna 76 Trump ya ce abin takaici ne ganin yadda rashin gaskiyar kafafen yada labaran ya wuce kima.
Donald Trump ya kuma zargi kafafen yada labarai musamman na kasar da yi wa wasu ‘yan tsiraru aiki.
Wannan dai ba shi ba ne karon farko da Trump ke sukar 'yan jarida ko shiga sai-in-sa da su tun bayan da ya soma jan ragamar mulkin Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu