Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU ta fitar da hasashen tattalin arzikinta na 2018

Tarayyar Turai ta fitar da hasashen ci gaban tattalin arzikinta na 2018, tare da bayyana cewa matakan farfado da tattalin arzikin kasashen nahiyar na kan hanya duk da adawa da ke fitowa daga gwamnatin Trump da kuma barazanar ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Tattalin arzikin kasashen Turai na fuskantar rashin tabbas fiye da shekarun baya
Tattalin arzikin kasashen Turai na fuskantar rashin tabbas fiye da shekarun baya REUTERS/Yves Herman
Talla

Tattalin arzikin kasashen Turai dai na fuskantar rashin tabbas fiye da shekarun baya inda bashi ya yi wa wasu mambobin Kasashen katutu.

Wannan ne dai karon farko a cikin shekaru 10 da hasashen ya nuna cewa tattalin arzikin mambobin kasashe Tarayyar Turai da ke amfani da kudirin euro 28 zai karu a hasashen ci gaban na shekaru 3.

Hasashen ci gaban tattalin arzikin ya nuna samun ci gaba da sama da kashi daya da rabi a 2017 tare da Karin samun ci gaba a 2018.

Hasashen dai ya sabawa wanda aka wallafa a watan Nuwamban 2016 wanda ya nuna samun ci gaba da kashi 1 da rabi a 2017.

Hasashen ya nuna cewa hatta kasar Girka tattalin arzikinta zai samu habbaka da kusan kashi 3 a 2017 sanna zai karu da sama da kashi 3 a 2018.

Wannan dai na zuwa duk da ficewar Birtaniya na yin barazana ga ci gaban tattalin arzikin Tarayyar Turai da kuma manufofin Trump da ke cin karo da muradun Turai.

Hasashen dai ya nuna cewa Barazanar Birtaniya da rashin tabbas daga manufofin Trump, na iya kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikin na kasashen na Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.