Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Amurka ta tabbatar da Sessions a matsayin Antoni Janar

Majalisar Dattijan Amurka ta tabbatar da na hannun daman Mista Trump, Jeff Sessions a matsayin sabon Antoni Janar na kasar, matakin da ke zuwa bayan muhawarar da majalisar ta tafka mai cike da rarrabuwar kawuna, kan batun kare hakkin dan'adam.

Sabon Antoni Janar na kasar Amurka Jeff Sessions
Sabon Antoni Janar na kasar Amurka Jeff Sessions REUTERS/Carlo Allegri/File Photo
Talla

A baya dai an taba haramtawa Mista Sessions damar zama alkalin kotun tarayya, sama da shekaru 30 da suka gabata, lokacin da aka zarge shi da nuna wariyar launin fata, zargin da ya sha musantawa.

Jeff Session ya zama sabon Antoni Janar a Amurka na 84 a zabensa da ‘yan majalisun suka yi, inda ya samu kuri’u 52 sama da 47 na masu adawa, an kuma samu dan Democrats guda, Joe Machin, da jefa masa kuri ‘a wanda ke wakiltar Yammacin Virginia.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya jim-ma yana sokar Democrats da haifar da cikas wajen amincewa nadin Mista Session kan lokaci, batun da ya bayyana a matsayin abin kunya.

Session, wanda ake gani zai taimakawa Trump wajen aiwatar da manufofinsa kan baki, shi ne mutum na 6 cikin 15 da aka tabbatar yanzu a gwamnatin shugaban.

Kuma yanzu aikinsa shi ne dawainiya da sashin shari’ar kasar mai ma’aikata dubu 113, wanda yanzu haka ake tafka muhawara kan irin matakan da shugaba Trump ke dauka, tun daga rantsar da shi zuwa yanzu, bayan umarnin datse ‘yan gudun hijira da bakin shiga kasar daga kasashen muslmi 7 da ke duniya.

A shekarar 1986 Sessions ya taɓa kiran Ƙungiyar Kare muradun bakakken fata ta kasar Amurka a matsayin "marar kishin kasa’’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.