Australia
Ana zargin shugabannin darikar katolika 7 da cin zarafin yara a Australia
Wani bincike da gwamnatin Australia ta gudanar, ya bayyana cewar kashi 7 na shugabanin mabiya darikar Katolika a kasar sun ci zarafin yara kanana tsakanin shekarar 1950 zuwa 2010 kuma babu wani mataki da aka dauka akai.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukumar binciken tace an gabatar da kararaki 4,444 na yadda shugabanin ke cin zarafin yara kanana yara amma kuma cocin yaki daukan mataki akai.
Gail Furness, lauyan dake jagorancin binciken yace sau da yawa idan an samu irin wannan zargi sai a sauyawa shugabanin wurin aiki maimakon hukunta su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu