Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa: Le Pen na Kamfen kamar na Trump

Shugabar jam’iyyar National Front ta masu kishin kasa a Faransa Marine Le Pen ta kaddamar da yakin neman zabenta mai yanayi da na Donald Trump da ya ba shi nasarar lashe zaben Amurka.

Marine Le Pen, 'Yar takarar Jam'iyyar FN masu kishin kasa a Faransa
Marine Le Pen, 'Yar takarar Jam'iyyar FN masu kishin kasa a Faransa REUTERS
Talla

“Faransa ce farko” shi ne taken yakin neman zaben Le Pen kamar yadda Trump ke cewa Amurka farko.

A jawabin da ta gabatar a jiya Lahadi a birnin Lyon bayan ta kaddamar da yakin neman zabenta, Le Pen ta ce abin da wasu ke ganin bai taba faruwa, sai ga shi yanzu kuma yana faruwa. Don haka a cewarta za ta lashe zaben Faransa kamar yadda Donald Trump ya zama shugaban Amurka.

Kuri’un ra’ayin jama’a dai sun nuna Le Pen za ta lashe zagaye na farko a zaben Faransa da za a gudanar a watan Afrilu.

‘Yar takarar da ke adawa da baki da musulmi, ta wallafa jerin manufofinta 144 ga Faransawa, da suka hada da ficewar kasar daga kungiyar kasashe masu amfani da kudin euro da kara kudaden haraji ga ma’aikatan kwadago baki da suka shigo Faransa.

Sannan ta yi alkawalin korar yan kasashen waje da aka kama da aikata laifi a Faransa.

Zaben Faransa dai zai ja hankalin duniya kamar na Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.