Isa ga babban shafi
Turkiya-Jamus

Erdogan ya maidawa Markel martani da kakkausan harshe

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyib Erdogan, ya maidawa shugabar Jamus Angela Markel martini da kakkausan harshe, jim kadan bayan wata tattaunawar karfafa dangantaka da suka yi.

Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan, tare da shugabar Jamus Agela Markel
Shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyib Erdogan, tare da shugabar Jamus Agela Markel REUTERS/Umit Bektas
Talla

Erdogan ya nuna fushinsa ne kan kalamin da Markel ta yi, na danganta ta`addanci da Musulunci, yayin wata ziyarar kwana guda a kasar.

Markel ta yi wannan furucin ne a lokacin da take jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin Jamus da Turkiya kan yaki da ta`addanci, da kuma murkushe tada kayar bayan mayakan kurdawa na PKK.

Kai tsaye cikin kaushi Erdogan ya maidawa Markel martanin cewa danganta musulunci da ta`addanci kuskure ne, duba da ma:anar Islam shi ne zaman lafiya, kuma hakan ba ya yiwa al`ummar Musulmi dadi, abinda Erdogan yace ba zai lamunta ba.

A baya dai Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya kaucewa yin amfani Kalmar Islamic Terrorism a turance da ke daganta Musulunci da ta:addanci, wanda Obaman ya ce addinin bai amince da shi ba.

Sai dai shugaban Amurkan a yanzu Donald Trump, yana alkanta addinin da ta:addanci, tare da sukar Obama bisa yadda ya kaucewa amfanin da Kalmar da ke alakanta musulunci da ta:addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.