Isa ga babban shafi
Canada

Mutum guda ne kawai dan ta'adda daga cikin 2 da aka kame

Yan sanda a Canada sun ce daya daga cikin mutane biyu da suka kame ne kawai dan bindigar da ake zargin ya bude wuta kan masu ibada a wani masallaci da ke birnin Quebec.

Masallacin Quebec da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa hari.
Masallacin Quebec da wasu 'yan ta'adda suka kaiwa hari. REUTERS/Mathieu Belanger
Talla

Yan sandan sun ce sun samu nasarar kame mutum guda ne, bayanda ya ya kira su da kansa ya kuma shaida musu inda yake, yayinda suka yi kuskuren kama mutum guda da suka yi zaton abokin maharin ne.

Mutane shida ‘yan bindigar suka halaka, yayinda suka raunata wasu 8, a lokacinda suka bude wuta kan masallata 50 da ke ibada.

A baya dai masallacin na Quebec ya taba fuskantar barazana da nuna kyama, a lokacin da wasu da ba’a san ko su waye ba suka ajiye kan alade a kofar masallacin, a cikin watan azumin da ya gabata, da yayi dai dai da watan Yunin shekarar 2016.

Harin ta’addancin kan masallacin na Quebec na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Canada ta sha alwashin karbar musulmi da ‘yan gudun hijira, biyo bayan dokar hanasu shiga Amurka da sabon shugaban kasar Donald Trump ya rattabawa hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.