Isa ga babban shafi
Amurka

An kame sama da mutane 90 a Washington

‘Yan sanda a birnin Washington sun kame sama da mutane 90 bisa samunsu da laifin lalata dukiya, yayin zanga zangar da suka gudanar don adawa da rantsar da sabon shugaban Amurka Donald Trump.

Barnar da masu zanga zangar adawa da Donald Trump suka yi a birnin Washington
Barnar da masu zanga zangar adawa da Donald Trump suka yi a birnin Washington REUTERS/Adrees Latif
Talla

Yayinda ake daf da fara bikin rantsuwar sabon shugaban kasar ne, arrangama da kaure tsakanin masu zanga zangar kimanin 500 da jifa da duwatsu da kuma ‘yan sanda, wadanda suka maida martani da harba hayaki mai sa hawaye.

Jifan da masu zanga zangar suka yi yayi sanadin fasa gilasan wani banki da ke wajen, da kuma shagunan saida kayayyaki.

‘Yan sanda guda biyu ne suka samu raunuka sakamakon aranngamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.