Isa ga babban shafi
Amurka

Kalaman Trump sun jefa shakku kan dangantakar Amurka da Turai

Shugabannin Turai na ci gaba da mayar wa da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da martani bayan ya ce Kungiyar tsaro ta NATO ba ta da wani amfani kuma Jamus ta yi kuskure wajen amincewa da ‘yan gudun hijra.

Donald Trump a zantawa da jaridar Bild ta kasar Jamus da jaridar Newyork Times ta Britaniya.
Donald Trump a zantawa da jaridar Bild ta kasar Jamus da jaridar Newyork Times ta Britaniya. RFI
Talla

Trump ya kuma soki Tarayyar Turai game da ficewar Birtaniya a kungiyar tare da tabo batun Nukiliyar Iran da ya yi barazanar rusawa.

Akwai yiyuwar Trump zai iya kulla yarjejeniya da Rasha da kuma sassauta takunkuman da Amurka ta kakaba ma ta.

Kalaman na Trump dai sun ja hankali musamman kasashen Turai da suke ganin zai sauya huldar Amurka da su.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.