Theresa May, zata kawo karshen yarjejeniyar cinakaiyya da kasashen turai?
Ana rade radin cewa fm kasar Britaniya uwargida Theresa May na shirin fitar da kasar daga cikin kasuwanci da ta jami’an costum da kasashen tarayyar turai, domin samun damar kula da daukacin kan iyakokin kasar, kamar yadda kafofin yada labaran kasar ta Britaniya suka ruwaito a yau lahadi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A jibi talata ne ake sa ran Firayi ministar ta Ingila Theresa May ta gabatar da jawabin da ake jira kan batun da ya shafi ficewar da kasar kwata kwata daga kungiyar taryyar turai.
Sai dai kuma fadar Downing Street ta yi tsokaci kan rade radin da kafofin yada labari ke yadawa, kan fitar da kasar daga cikin huldar kasuwanci da Kostom tsakaninta da kasashen turai, al’umarin da fadar ba gaskiya bane hasashe ne kawai na yan jaridu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu