Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Trump na shirin fidda rahoto kan kutsen Rasha a zaben Amurka

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya yi alkawarin fitar da rahoto game da zarge-zargen kutsen Rasha a lokacin zaben kasar da aka gudanar a cikin watan Nuwamban bara.

Shugaban Amurka mai jiran gado  Donald Trump.
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump. REUTERS/Carlo Allegri/Files
Talla

A wasu sakwanni da ya fitar ta kafar Twitter, Mr. Trump ya ce, nan da kwanaki 90 ne zai fitar da rahoto kan zargin da ya ke ganin wasu bata-garin ‘yan siyasa ne suka kirkire shi.

Hukumar leken asirin Amurka ce dai ta zargi Rasha da yin kutse a sakwannin Imel din wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar Democrat ta su Hillary Clinton da Barack Obama.

Ana ganin rahoton zai kawo karshen danbarwar da ke a tsakanin Rasha da Amurka game da zaben shugabancin kasar ta Amurkada ake zargin Rasha da taka rawar da ta bai wa Trump Nasara a zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.