Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 27/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 27/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 27/02 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 27/02 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 27/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 27/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Turai

Jamus za ta mayar da 'yan ci-rani Girka

media Sanyin hunturu ya addabi 'Yan ci-rani a Kasashen Turai Foto: AFP

Kasar Jamus ta ce daga watan Mayun shekara 2017, za ta dawo da shirin mayar da sabbin 'yan gudun hijira da suka shiga kasar zuwa Girka, bayan shafe shekaru 5 da dakatar da shirin sakamakon rashin kyawun yanayi a sansanonin Girka.

Cikin tsohon tsarin da ake kira da ''Dublin'' dole ne 'yan gudun hijira su fara neman mafaka a kasar da suka fara shiga, da suka hadar da Italiya da Bulgaria da kuma ita kan ta Girka da masu gudun hijirar suka fi tururuwa.

To sai dai kuma Girka ta soki matakin na Jamus inda ta ce, hakan zai dora nauyi matuka kan kasashen da 'yan gudun hijirar suka fara isa.

Yanzu haka dai akwai akalla 'yan gudun hijira kimanin 62,000 da ke kasar ta Girka, babu kuma ranar barinsu kasar sakamakon rufe iyakoki da kasashen da ke makwabtaka da ita suka yi.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure