Isa ga babban shafi
Birtaniya

Yaran Calais sun dauki matakin shari’a akan Birtaniya

Kananan Yara ‘yan gudun hijira sun dauki matakin shari'a akan gwamnatin Birtaniya a  saboda yadda ta nuna halin-ko-in-kula a lokacin da suke neman mafaka a kasar, bayan shafe watanni a dajin Calais na Faransa.

Sansanin 'yan gudun hijra da ke Calais na kasar Faransa.
Sansanin 'yan gudun hijra da ke Calais na kasar Faransa. DENIS CHARLET / AFP
Talla

Kananan yaran sun dauki wannan matakin ne don kalubalantar yadda gwamnatin Birtaniya ta ki daraja kokensu a lokacin da suke cikin halin damuwa a dajin Calais na Faransa, kamar yadda lauyoyin da ke kare su suka sanar.

Yaran dai sun zargi Ministan cikin gidan Birtaniya Amber Rudd da kin mutunta sashi na 67 da ke kunshe a cikin dokar gudun hijira da ta bada damar bai wa kananan yara marasa galihu mafaka, musamman wadanda ke fuskantar barazanar fyade.

Kazalika yaran sun koka kan yadda kasar ta yi watsi da takardun da suka gabatar a hukumance don neman izinin samun mafaka.

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne, gwamnatin Birtaniya ta amince ta karbi yaran ‘yan gudun hijirar da shekarunsu bai haura 15 ba da kuma ke cikin wani hali a sansanin Calais, bayan ta sha matsin lamba sakamakon rashin daukan matsalar ‘yan gudun hijirar da muhimmanci.

Kimanin yara 750 ne suka shiga Birtaniya daga sansanin Calais a cikin wannan shekarar kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.