Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha za ta tsaurara dokoki kan barasa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar da umarnin tsaurara dokoki dangane da yadda ake sarrafawa da kuma shan barasa a kasar, bayan da aka tabbatar da mutuwar mutane 62 sakamakon sha wata gurbatacciyar barasa a yankin Serberia.

Wani nau'i na barasar da ake sarrafawa a Rasha
Wani nau'i na barasar da ake sarrafawa a Rasha ANDREY SMIRNOV / AFP
Talla

Shugaba Putin ya umarci a samar da sabbin dokokin ne kafin watan Yulin shekara mai zuwa dangane da yadda za a sayar da kuma sarrafa barasa a kasar, kazalika dokar za ta shafi wasu kayayyaki da suka hada da turare da sabulu da kuma sinadiran tsaftace gidaje wadanda su ma ke da hadin barasa a cikinsu.

Har ila yau, sabbin dokoki za su shafi sinadirai da kuma magungunan da ake ake sarrafawa domin kula da lafiyar dabbobi ba wai jama'a kawai ba.

Dokokin da ake neman kafawa za su kasance masu tsauri wanda hakan zai sa a samu raguwar mashaya barasa a kasar, kamar yadda fadar Kremlin ta bayyana.

Daukar matakin dai ya biyo bayan asarar rayukan mutane 62 ne da aka sama a yankin Serberia tsakanin shekaranjiya asabar zuwa laraba, bayan da suka kwankwadi wata barasa da aka ce an yi ma ta mugun hadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.