Isa ga babban shafi
Poland

'Yan Majalisar Poland sun gaza cimma sulhu da gwamnati

‘Yan Majalisar kasar Poland 24 daga babbar jam’iyyar adawar kasar, sun kara wa’adin zaman dirshan da suke yi a zauren majalisar kasar, domin nuna adawa da matakin gwamnati na kayyade ‘yan jaridu da zasu rika shiga zauren majalisar.

Zanga zangar da ke gudana a Poland
Zanga zangar da ke gudana a Poland
Talla

Yan Majalisar sun dauki matakin ne bayan gaza cimma matsaya yau Lahadi tsakaninsu da gwamnati kan matakin da suka ce ba zasu lamunta ba, duk da kokarin Shugaban kasar Andrzej Duda na kawo karshen takaddamar.

Matakin kayyade yawan yan jaridun da zasu rika daukar rahoton abinda ke wakana a majalisar kasar ya haifar da zanga zangar da aka jima ba’aga irinta ba a kasar ta Poland, sakamakon bazuwar zanga zanga zuwa sassan kasar.

A baya bayannan ne dai gwamnatin Poland na fuskantar matsin lamba sakamakon matakan da take cigaba da dauka na neman samun cikakken iko kan kafafen yada labaran kasar, kamar yadda 'yan adawa dama wasu kungiyoyin masu zaman kansu ke zargi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.