Isa ga babban shafi
Rasha-Wasanni

An bankado laifukan 'yan wasan Rasha sama da 1000

Hukumar da ke yaki da shan kwayoyin kara kuzari tsakanin ‘yan wasa ta Duniya, WADA, ta ce sama da ‘yan wasan kasar Rasha 1000 ne suka amfana, ko kuma ke da hannu dumu cikin boye almundahanar tu’ammuli da kwayoyi tsawon lokaci.

Tawagar 'yan wasan motsa jiki ta kasar Rasha
Tawagar 'yan wasan motsa jiki ta kasar Rasha
Talla

Alkaluman na kunshe cikin wani rahoto da hukumar ta wallafa, wanda sanannen lauyan wasanni dan kasar Canada Richard McLaren ya binciko, domin samar da karin bayani kan zargin da akewa kasar Rasha da hannu wajen goyon bayan ‘yan wasanta su yi amfani da kwayoyin karin kuzari.

Rahoton ya ce ‘yan wasan na Rasha hadi da hukumomin kasar sun yi nasarar boye amfani da kwayoyi a yayin wasannin Olympics da suka gudana a shekara ta 2012 a birnin London, 2014 a birnin Sochi, sai kuma a lokacin gasar wasannin motsa jiki ta Duniya da akayi a shekara da 2013.

Raohoton ya kuma kara da cewa kimanin hukumomin kula da wasannin daban daban har guda 30 na Rasha aka samu da laifin aikata almundahanar, ciki har da hukumar kwallon kafa ta kasar.

Sai dai a martaninsu, jami’an Rasha sun ce babu wata sahihiyar hujjar da ke nuna cewa gwamnatin kasar ta goyi bayan ‘yan wasan da suka aikata laifukan tu’ammuli da kwayoyin.

‘Yar wasan Rasha Yulia Stepanova da ta fara fallasa wannan badakala, a baya ta taba nadar muryoyin ‘yan wasan Rasha da masu horar da su, yayin da suke bayanin yadda kwayoyi ke taimaka musu wajen samun Karin kuzari yayin fafatawa a wasanni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.