Isa ga babban shafi
Iraqi

IS ta nuna bidiyon dan jaridar Birtaniya da ta sace

Wani hoton bidiyo da kungiyar IS ta fitar, ya nuna John Cantile, dan jaridar Birtaniya da aka sace shekaru hudu da suka gabata a Syria.

Dan jarida  James Foley da kungiyar IS ta hallaka har lahira
Dan jarida James Foley da kungiyar IS ta hallaka har lahira REUTERS/Social Media Website via REUTERS TV
Talla

Hoton wanda aka dauka a birnin Mosul na Iraqi, ya nuna Cantile a cikin mawuyacin hali, in da kuma yake magana da harshen Ingilishi.

A cikin watan Nuwamban shekarar 2012 ne aka sace dan jaridar da abokin aikinsa James Foley a dai dai lokacin da suke daukan rahoton yakin Syria.

Sai dai Tuni kungiyar ta IS mai da’awar jihadi ta aika da Foley har lahira.

Bidiyon wanda kafar Amaq ta watsa, bai bayyana ranar da aka dauki hoton ba amma ana kyautata zaton cewa, an dauki hoton ne a ‘yan makwannin baya-bayan na, saboda wata gada da ba a jima da rusa ta ba da kuma ake kallon ta a rushe a bidiyon.

Rundunar da Amurka ke jagoranta ta rusa gadoji da dama a birnin Mosul a yayin taimaka wa dakarun Iraqi wajen fada da IS.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne, dakarun suka kaddamar da farmaki da nufin kwace birnin mai cike da tarihi daga hannun kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.