An hana motoci fitowa a Paris saboda yanayi
Birnin Paris na kasar Faransa na fama da matsalar gurbacewar yanayi a dai dai lokacin da sanyin hunturu ya fara, lamarin da ya tilasta wa hukumomi daukar matakin hana rabin motocin da ke birnin fitowa kan tituna.
Wallafawa ranar:
Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru10 da ake fuskantar irin wannan matsala a birnin, in da a yau Alhamis kwanaki uku kenan da daukar matakin hana rabin motocin birnin fitowa .
Gurbacewar yanayin ta haifar da jiri da ciwon ido da kuma mura ga jama’a, to sai dai duk da wadannan matsaloli da ake fama da su a birnin, mazaunansa na nuna adawa da matakan da ake dauka na hana zirga-zirgar.
A wani mataki na magance yiyuwar karancin ababan hawa, gwmanati ta samar da motoci da ke jigilar jama’a kyauta a tsawon wadannan kwanaki.
Tun kafin lokacin tsanantar hunturun bisa ga al’ada, tuni sanyi ya yi matukar muni a birnin da kuma wasu yankuna na Faransa, in da kuma iska ta daina kadawa, yayin da haske ya ragu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu