Isa ga babban shafi
Haiti

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi afuwar al'ummar Haiti

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya nemi gafarar al’ummar kasar Haiti saboda zargin kai cutar kwalara kasar, da ake yiwa dakarun samar da zaman lafiya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Talla

Ban yace Majalisar bata yi kokari sosai wajen magance matsalar cutar lokacin da ta barke ba, saboda haka a madadin Majalisar yana neman gafarar al’ummar Haiti.

Shaidu dai sun nuna cewar jami’an tsaron kasar Nepal ne suka kai cutar Haiti wadda ta kashe mutane sama da 9,000.

Bincike ya tabbatar da cewa dakarun Majalisar Dinkin Duniyar sun zauna ne a wata cibiya dake kusa kogi, wanda kuma gurbataccen ruwa daga cibiyar ke kwaranya cikinsa lamarin da yasa kasha na farko na mutanen da suka kamu da cutar amai da gudawa, sune wadanda ke rayuwa a kusa da kogin.

Hakan ta sa masana lafiya suka bi diddigin yadda al’amarin ya auku kafin daga bisani su tabbatar da zargin da ake yiwa jami’an na Majalisar Dinkin Duniya.

A shekara ta 1999, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya na waccan lokacin Kofi Annan ya nemi afuwakan yadda Majalisar ta gaza wajen kare fararen hula yayin kazamin kisan kare dangin da ya auku Ruwanda shekaru biyar bayan aukuwar rikicin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.