Isa ga babban shafi
Bulgaria

Arrangama tsakanin 'yan gudun hijira da jami'an tsaro a Bulgaria

‘Yan sanda a kasar Bulgaria, sun yi amfani da barkonon tsohuwa hadi da ruwan zafi domin tarwatsa dandazon ‘yan gudun hijira da ke zanga-zanga ta rashin yarda da matakin hukumomin kasar, na hana su motsawa daga sansanin da aka ajiye su, har sai an tantance lafiyarsu.

'Yan sandan Bulgaria yayin arrangama da 'yan gudun hijira da ke sansanin Harmanli
'Yan sandan Bulgaria yayin arrangama da 'yan gudun hijira da ke sansanin Harmanli
Talla

Akalla ‘yan sanda 6 suka samu munanan raunuka sakamakon arrangamar da suka yi da ‘yan gudun hijirar da yawansu ya kai, 1,500, a sansanin Harmanli da ke kan iyakar Bulgaria da Turkiya.

Hukumomin Bulgaria sun dauki matakin dakatar fitar masu gudun hijirar kimanin 3,000, daga sansanin na Harmanli, saboda fargabar an samu bullar wata cuta ta fata, da ka iya yaduwa tsakanin al’ummah.

An dai zargi masu zanga zangar da lalata gine gine da dama a sansanin, ta hanyar cinnna musu wuta, baya ga rotse da duwatsu, da suka rika yiwa jami’an ‘yan sanda.

Tun a shekarar da ta gabata gwamnatin Bulgaria ta gina katafariyar katanga kan iyakarta da Turkiya, domin rage kwararar ‘yan gudun hijira cikin kasar.

Kawo yanzu 'yan gudun hijira 17,000 hukumomin kasar suka tsare a watanni goma na shekarar 2016 da muke ciki.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.